Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: an haramta saye da kuma sayar da kur'ani mai girma bugon jamai'ar Azhar a fadin Palsdinu saboda yana kumshe da kurakure wajan bugashi .An nakalto daga majiyar kusa da FELESTEEN cewa; Sheikh Muhamamd Husein babban mai fitar da fatawa a birnin kudus da kuma Palasdinu baki daya kuma shugaban komitin koli na masu fitar da fatawa a Palsdinu ya fitar da wata fatawa a cikin wani bayani wanda ya bukaci dakatar das aye da kuma sayar da kur'ani mai girma bugon jami'ar azhar saboda yana kumshe da kurakure . Sheikh Muhammad Huseini a ranar sha uku ga watan Farvardin na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya ne ya fitar da wannan bayanin cewa a shafi na dari uku da uku a cikin aya ta tamanin da hudu na suratul Kahafi akwai matsala da kuskuren bugo . Kuma wanann bas hi ne karon farko da ake samin matsalar da kuskuren buga kur'ani a wannan jami'a ta Azhar duk da fice da sunan da ta yi wajan yada ilimi addini a fadin duniya.
976949