Bangaren siyasa da zaman takewa: ofishin da ke kula da harkokin da suka shafi yada al'adun jamhuriyar musulunci ta Iran ya yi nuni da cewa: Mai martaba Zainab (AS) ta hanyar hakuri da tsayin daka da nuna jarunta ta yada tsayi da Imam Huseini (AS) yayi na yakar zalunci.
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; ofishin da ke kula da harkokin da suka shafi yada al'adun jamhuriyar musulunci ta Iran ya yi nuni da cewa: Mai martaba Zainab (AS) ta hanyar hakuri da tsayin daka da nuna jarunta ta yada tsayi da Imam Huseini (AS) yayi na yakar zalunci.Muhammad Rida Kazlasfali mai kula da ofishin yada al'adun jamhuriyar musulunci ta Iran a kasae Sera leyon a daidai lokacin bukin tuni da zagayowar irin wannan rana ta haifuwar Hadarat Zainab (AS) ya bayyana cewa; Hadarat Zainab (AS) bayan ta jagoranci tawagar wadanda suka komo daga filin dagar Ashura bayan abin bakin ciki da zaluncin day a faru a ranar goma ga watan Muharram ta kula da maras lafiya da wadanda aka jikata kuma ta tsaya tsayin daga tashi tsaye wajan ganin ta bayyanawa sauran al'ummomin duniya hakikanin abin day a faru dab akin zalunci na rashin tausayi da aka nuna wa Imam Huseini (AS) da sahabbansa da kuma iyalan gidansa a wannan bakar rana a wannan guri na karbala da kuma sauran abubuwan da suka faru bayan wannan rana.
977697