IQNA

An Kaddamar Da Wani Salon Koyar da Kur'ani Mai Girma Ta Hanyar Fim A Tataristan

17:22 - April 05, 2012
Lambar Labari: 2298373
Bangaren harkokin kur'ani mai girma: hukumar da ke kula da gidan radio da talbijin na jamhuriyar Tataristan ta shirya hanyar koyan karatun kur'ani da harda kuma ta bayyana cewa a shirye take ta fara watsa wag a dukan mai bukata a fadin kasar.




Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; hukumar da ke kula da gidan radio da talbijin na jamhuriyar Tataristan ta shirya hanyar koyan karatun kur'ani da harda kuma ta bayyana cewa a shirye take ta fara watsa wag a dukan mai bukata a fadin kasar. Ofishin da ke bin diddigi da lura da harkoki da lamuran da suka shafi musulmi a fadin kasar a ranar sha hudu ga watan farvardin na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in da daya hijira shamsiya ya bada wannan labarin cewa; wannan fim din wani jan kokari da himma ne na hukumar da ke kula da radiyo da talbijin a kasar tare da tuntuba da taimakon jami'ar musulunci ta Rasha musamman bangaren tarbiyartar day aye makaranta kur'ani da mahardata kur'ani mai girma a wannan jami'ar da ke birnin Kazan na kasar. Kuma tuni aka shira a ranar sha takwas ga watan farvardin na shekara ta dubu daya dari uku da tis'in hijira shamsiya da misalign karfe tara da minti biyar agogon kasar kamar yadda aka shirya gidan talbijin na Rasha a yankin Tataristan zai fara watsa wannanfim na koyar da kur'ani mai girma.

977904
captcha