Bangaren kasa da kasa; a ranar ashirin ga watan Farvardin na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya aka kawo karshen gasar karatun kur'ani mai girma gay an jami'a irakiyawa a birnin Karbala kuma Darul Kur'ani karim da ke karkashin hubbarin Imam Huseini (AS) a garin Karbala ya dauki dawainiya da hidimar gudanar da wannan gasa da bada horon karatun kur'ani ga yan jami'ar.
Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kuma da harkokin kur'ani mai girmna a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: a ranar ashirin ga watan Farvardin na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya aka kawo karshen gasar karatun kur'ani mai girma gay an jami'a irakiyawa a birnin Karbala kuma Darul Kur'ani karim da ke karkashin hubbarin Imam Huseini (AS) a garin Karbala ya dauki dawainiya da hidimar gudanar da wannan gasa da bada horon karatun kur'ani ga yan jami'ar. Wannan bada horo dai yana daga cikin jerin shirye-shiryen bada horo da shirya gasar karatun kur'ani mai girma gay an jami'a Irakiyawa a fadin kasar ta iraki .Kuma taron rufe wannan gasar an gudanar da shi ne babban dakin gudanar da taro na Khatamul Annabiya da ke cikin hubbarin mai tsarki na imam Huseini (AS) kuma an samu halartar wakilan Hubbaran na imam Huseini (AS) da hadarat Abas (AS) da kuma na wakilan ma'aikatar bada ilimi mai zurfi da tarbiya a Iraki da kuma adaddi mai yawan gaske na malamai day an jami'a daga jami'o'I daban daban na Irakin da suka halarci gurin wannan taro.
981417