Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: karkashin shirin raba kur'anai dmiliyan ashirin da biyar a kasar Jamus ga wadanda ba musulmi ba a wannan kasar tuni aka bada da raba kur'anai dubu dari uku kyauta ga mabukata a wannan kasa ta yammacin turai.An nakalto daga majiyar labarai ta mooslym cewa; karkashin shirin nan na Ikra'a wato kayi karatu da Ibrahim Abu naji musulmi dan asalin kasar Palsdinu da ke zaune a birnin Balin na kasar Jamus ya kirkoro na raba kur'anai miliyan ashirin da biyar ga duk wani wanda yake son wannan littafi mai tsarki kuma wanda yake bukatar ya kasance ba musulmi ba tuni ya raba kur'ania dubu dari uku gay an kasar ta Jamus kuma wadannan kur'ani ne da aka tarjama a cikin harshen jamusanci kuma wannan na nuni da yadda mutane ke kara nuna kauna da kur'ani mai tsarki ,kuma a bullo da wannan shiri ne a shekara ta dubu biyu da goma sha daya miladiya.
984489