Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: An kawo karshe da kammala gasar karatun kur'ani mai girma da harda musamman ga mata a garin Kazan fadar mulkin Tataristan kuma wannan gasar karatun kur'ani mai tsarki ta samu kayatarwa da cimma nasara mai girma. A wajan gudanarwa musamman a lokacin fara wannan gasar da kuma lokacin kammala wannan gasar an samu halartar manyan baki kama daga wakilan gwamnati da na jam'iyun siyasa da na addinin musulunci da na kungiyoyin addini da mahardata da uwayan yara da suka halarci gurin wannan gasar karatun kur'ani mai tsarki kuma sun bayyana gamsuwarsu da yadda aka tsara da shirya wannan gasar da kuma yadda aka cimma nasara daga farko har zuwa karshen wannan gasar kuma hatta a hirarraki da tattaunawar da aka yi da wadanda suka halarci wannan gasar sun nuna farin ciki da gamsuwa kan yadda aka shirya wannan gasar.
984644