IQNA

Fara Gasar Kur'ani A Fadin Mauritaniya

18:31 - April 21, 2012
Lambar Labari: 2309324
Bangaren kasa da kasa; an fara gasar karatun kur'ani da hardada kuma Tajwidi gami da tafsirin kur'ani mai girma a ranar alhamis talatin da daya ga watan farvardin na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya da gidan radiyon Kur'ani na Mauritaniya ya shirya a babban masallacin birnin Nuwakcit fadar mulkin kasar ta Mauritaniya.



Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: an fara gasar karatun kur'ani da hardada kuma Tajwidi gami da tafsirin kur'ani mai girma a ranar alhamis talatin da daya ga watan farvardin na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya da gidan radiyon Kur'ani na Mauritaniya ya shirya a babban masallacin birnin Nuwakcit fadar mulkin kasar ta Mauritaniya.An nakalto daga majiyar labarai ta Aklhabar mauritaniya cewa wannan gasar ta aka fara a ranar alhamis ana gudanar da ita ne da zummar zabar gwarzon wannan shekara da zai wakilci kasar a gasar karatun kur'ani ta kasa da kasa da za a yi kuma za a kwashe makonni biyu ana ci gaba da gudanar da wannan gasar. Kuma shi wannan ya yi nasara a wannan gasar shi ne zai wakilci kasar ta Mauriytaniya a gasar kasa da kasa da ake gudanarwa kowace shekara a kasashe kamar : Masar,Jamhuriyar musulunci ta Iran ,Marokko,Aljazair ,Tunusiya,Libiya.Koweiti, Sudan, Saudiya, Hadeddiyar daular larabawa, Iraki ,Jodan da kuma malaishiya.Kuma mahardata kur'ani dari da goma sha shidda ne ke fafatawa da juna a wannan gasar karatun kur'ani ta kasar Mauritaniya day a hada da mata biyar.

989569
captcha