IQNA

Koyar Da Kur'ani A Lardin Gur Na Kasar Afganistan

17:51 - April 23, 2012
Lambar Labari: 2311036
Bangaren harkokin kur'ani : a kokari da himmar ciyar da harkokin kur'ani da ilimin kur'ani da kuma na addinin musulunci da kuma al'adu irin na addinin musulunci a kafa wasu cibiyoyi har guda shida na koyar da kur'ani mai girma a lardin Gur na kasar Afganistan.



Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: a kokari da himmar ciyar da harkokin kur'ani da ilimin kur'ani da kuma na addinin musulunci da kuma al'adu irin na addinin musulunci a kafa wasu cibiyoyi har guda shida na koyar da kur'ani mai girma a lardin Gur na kasar Afganistan. Shugabannin da ke kula da harkokin addini da bada horo ne suka yanke shawara ta shirya wannan tsari na koyar da kur'ani mai tsarki a wannan yanki na Gur a kasar ta Afganistan kuma kimanin talibai dari hudu da hamsin ne daga cikin matasa da yara a kauyukan L'al da sarjangal a lardinGur day a hada mata da yara maza suke halartar wannan zangon koyarwa kuma suna halartar wannan zangon karatu ne a cikin tsari da aka yi da rarrabawa a cikin ajiyoyin guda shidda.
990933

captcha