Bangaren kasa da kasa: yara kanana dari daya ne mahardata kur'ani mai girma a ranar sha daya ga watan Ordebehesht na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya za a girmama a wani taro na musamman da hadin guiwar kungiyoyin bayar da agaji na Alauraman na kasar Masar suka dauki dawainiyar gudanarwa a cibiyar musulunci ta jami'ar Azhar a kasar Masar.
Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musuluncin ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: yara kanana dari daya ne mahardata kur'ani mai girma a ranar sha daya ga watan Ordebehesht na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya za a girmama a wani taro na musamman da hadin guiwar kungiyoyin bayar da agaji na Alauraman na kasar Masar suka dauki dawainiyar gudanarwa a cibiyar musulunci ta jami'ar Azhar a kasar Masar. Bayan an nakalto daga jaridar Alyaum Sabi' da ake a kasar Masar cewa a wani bukin na musamman za a girmama yara kanana dari mahardata kur'ani mai girma kuma yaran da suka rasa uwayansu wato marayu kuma sun fito ne daga yankuna da bangarori daban daban na fadin kasar Masar kuma suka karatun kur'ani mai girma ne a karkashin wannan cibiya ta kur'ani da ke gudanar da ayyukanta karkashin jami'ar Azhar. Wannan buki na girmama yara kanana mahardata kur'ani mai girma a wannan rana an bawa taken ranar marayu a fadin kasar Masar kuma Ahmad Aldayib Shekhul Azhar ne zai girmama wadannan kananan yara kuma malaman jami'ar azhar da dama ne za su halarci wannan taro kuma za a bawa kowane yaro dubu dari na Janiye kudin kasar ta Masar. Burin wannan buki na jinjinawa yara kanana mahardata kur'ani mai girma shi ne kara jan hankali da kara sawa yara .matasa da manyan rungumar wannan hanya ta harda da karatun kur'ani mai girma.
991704