Bangaren kasa da kasa: babban sakataren kungiyar gwagwarmaya a kasar Labanon Hizbullah a ranar biyar ga watan Khurdad na wannan shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in da daya hijira shamsiya zai gabatar da jawabi ta hanyar shafin shafin Internet na tunawa ranar da a irinta ce aka yantar da kuduncin kasar Labanon kuma zai gabatar da wannan jawabi ne a bint Jabil.
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin da suka shafi kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; babban sakataren kungiyar gwagwarmaya a kasar Labanon Hizbullah a ranar biyar ga watan Khurdad na wannan shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in da daya hijira shamsiya zai gabatar da jawabi ta hanyar shafin shafin Internet na tunawa ranar da a irinta ce aka yantar da kuduncin kasar Labanon kuma zai gabatar da wannan jawabi ne a bint Jabil.A shekara ta dubu biyu miladiya ne a rana irin wannan dakarun gwagwarmaya na kungiyar Hizbullahi suka yantar da yankin kuduncin kasar ta labanon bayan sun nuna tsayin daka da kishin kasa da addini na kawo karshen mamaye da zalunci da danniyar sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila .Kuma ba wa kawai ga kungiyar Hizbullahi da dakarun gwagwarmaya na wannan kungiya kawai ba wannan rana da nasara tana da muhimmancin gaske ga al'ummar kasar da kuma gwamnatin musamman idan aka yi la'akarin da zaluncin Haramtacciyar kasar Isra'ila a yankin.
1006447