IQNA

A Wannan Litinin Din Ce Za A kammala Bincike Da Ake Kan Tarjamar kur'ani

16:35 - May 20, 2012
Lambar Labari: 2330090
Bangaren kasa da kasa;A wannan litinin din daya ga watan Khurdad na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in da daya hijira shamsiya a jami'ar ilimi da lura da harkokin da suka shafi kur'ani mai girma za a gudanar da wani zama na bincike da neman kawo gyara a cikin tarjamomin da ake yin a kur'ani mai girma a cikin yarukan Spaniyanci da Hausa da mu'assisar tarjamarWahayi ta ke gudanarawa .



Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin da suka shafi kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: A wannan litinin din daya ga watan Khurdad na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in da daya hijira shamsiya a jami'ar ilimi da lura da harkokin da suka shafi kur'ani mai girma za a gudanar da wani zama na bincike da neman kawo gyara a cikin tarjamomin da ake yin a kur'ani mai girma a cikin yarukan Spaniyanci da Hausa da mu'assisar tarjamarWahayi ta ke gudanarawa .A wannan zaman za a samu halartar hujjatul Islam walmuslim Muhammad Nakdi shugaban zartarwa na mu'assisar tarjamar wahayi da kuma Tidjani Malam lawali wani mai bincike kan abubuwan da suka shafi kur'ani da kuma Ali Faizulllahi mamba a komitin ilimi na jami'ar Tehran kuma shugaban bangaren harshen Spaniyanci a jami'ar da kuma Ma'asume Yazdan Panah mai bincike kuma wadda ta tarjama kur'ani mai girma zuwa harshen turancin Ingilishi da farisanci kuma wannan zaman za a gudanar da shi a wannan rana da misalign karfe goma na safe zuwa karfe shabiyu dakin taro na shahid Mufatih da ke kan titin Hafiz da kuma titin Janar Sakhayi a kuma da ma'aikatar tsaro da ke birnin Tehran. Wannanshi ne jerin zama irinsa na biyar da bangaren tarjamar kur'ani na kasashen waje tare da hadin guiwar kamfanin da ke kula da harkokin kur'ani a nan Jamhuriyar musulunci ta Iran Ikna da kuma jami'ar ilimi da fahimtar kur'ani mai girma suka shirya. A wajan wannan taron akwai masana da mashahuran masu bincike da nazari a lamurran da suka shafi kur'ani mai girma da za su halarta da yin bayanai kan abubuwan da suka shafi bincike da tarjamar kur'ani mai girma.
1011084
captcha