Bangaren kasa da kasa:Muhammad Mursi sabon shugaban kasar Masar ya bayyana cewa: Masar za ta ci gaba da kasancewa tare da al'ummar Palasdinu har zuwa lokacin da al'ummar Palasdinu za ta samun hakkokinta baki daya.
Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin da suka shafi kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: Muhammad Mursi sabon shugaban kasar Masar ya bayyana cewa: Masar za ta ci gaba da kasancewa tare da al'ummar Palasdinu har zuwa lokacin da al'ummar Palasdinu za ta samun hakkokinta baki daya.Majiyar labarai ta Palesdine Info ya watsa rahon cewa : a ranar asabar goma ga watan Tir na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in da daya hijira shamsiya a cikin jawabin da sabon shugaban kasar ta Masar Mursi ya gabatar a daidai lokacin da ake shan laya a jami'ar Alkahira ya bayyana cewa; kasar masar za ta ci gaba da kasancewa tare da al'ummar Palsdinu kuma y ace har sai al'ummar Palasdinu sun kwato yancinsu baki daya kuma zai ci gaba da ganin ya kawo sulhu a tsakanin kungiyoyi da al'ummomin Palasdinu.
1041831