IQNA

Nazari Kan Saka Hannayen Jari A Cikin Kamfanonin Kasar Masar

11:50 - September 10, 2012
Lambar Labari: 2408743
Bangaren kasa da kasa, ana shirin gudanar da wani zaman taro domin yin nazari kan batun saka hannayen jari a cikin kamfanonin kasar Masar domin farfado da sauran harkokin da suka kama hanyar durkushewa a kasar ta fuskacin kasuwanci da kuma harkokin banki kamar dai yadda bangaren kula da lamurran hannayen jari na kasar ya sanar.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo, cewa ana shirin gudanar da wani zaman taro domin yin nazari kan batun saka hannayen jari a cikin kamfanonin kasar Masar domin farfado da sauran harkokin da suka kama hanyar durkushewa a kasar ta fuskacin kasuwanci da kuma harkokin banki kamar dai yadda bangaren kula da lamurran hannayen jari na kasar ya sanar a jiya.
A bangare guda kuma an gudanar da wata zanga-zanga a cikin birnin Alkahira na kasar Masar domin nuna rashin amincewa da salon mulkin Muhammad Morsi tare da kasa aiwatar da abubuwan da ya yi wa mutane alkawali a lokacin da yake neman kuri'arsu. Rahotanni daga birnin Alkahira sun tabbatar da cewa masu zanga-zangar sun yi ta rera taken nuna rashin amincewa da mulkin Morsi, tare da daga hotunan tsohon shugaban kasar Jamal Abdul-nasir a matsayin wata alama ta kishin larabci da kuma kiyayya da kasashen yamma da haramtacciyar kasar Isra'ila.
Mohammad Morsi wanda ya lashe zaben shugaban kasar Masar da kusan kashi 52% karkashin inuwar kungiyar Ikhwanul Muslim, ya fara shan kakkausar suka daga wani bangare na al'ummar kasar Masar, musamman dangane da yadda kasar Masar ta ci gaba da gudanar da alakarta da haramtacciyar kasar Isra'ila ba tare da wani canji ba, duk kuwa da irin alkawalin da ya dauka na yin nazari kan dangantakar Masar da Isra'ila da kuma batun taimaka ma palastinawa, wanda a halin bayan darewa kan kujerar shugabanci, duk wadannan abubuwa ba su cikin abin da ya sanya a gaba, maimakon haka ma a makon da ya gabata ne ya aike da jakadansa zuwa haramtacciyar kasar Isra'ila.
1094044
captcha