
Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Akhbar Libiyah cewa gobe ne za a fara gudanar da wata gasar hardar kur’ani mai tsarki da kyautata tajwidinsa a jami’ar Asmariyyah dake garin Sabha da ke kudancin kasar Libya da nufin karfafa daliban kur’ani.
Bayanin ya ci gaba da cewa hardar za ta kunshi juzu’I na 30 haka nan kuma yan kasa da shekaru 10 za su yi harda ne kawai zuwa izihin tabarak, juzu’I na 29 kuwa zai kebanci yan kasa da shekaru 12 ne, kamar yadda juzu’I na 28 zai kebancinci yan shekara 15, har zuwa ‘yan shekaru 20, kamar yadda juzui na 24 zai hada da bangarori daban-daban na shekaru.
Wannan dai tana cikin muhimman ayyukan da jami’ar ta fara aiwatarwa da nufin karfafa harkokin kur’ani mai tsarki a kasar, wadda a halin yanzu take fama da matsaloli na tsaro da tashin hankali, sakamakon abin da yake faruwa na yaduwar yan ta’adda da suke dauke da muggan makamai musamman ma a yankunan gabacin kasar.
2612683