Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na shafaq News cewa daesh sun fara yin amfani da wani sabon salo na munanan ayyukansu wajen saka bam a cikin masallatai domin kashe musulmi a lokacin salla, ta hanyar saka bam din a cikin kwafin kur’ani tare da ajiye shi a cikin masallaci.
Bayanai sun ce akalla mutane talatin da bakawai ne su ka rasa rayukansu a wani jerin hare-haren ta'addanci a masallatan 'yan shi'a a kasar Iraki. Rahotanni daga kasar ta Iraki sun ambaci cewa an kai hare-haren ne a cikin masallatan kamaliyya da Za'afaraniyya da manaduqus-sha'ab wanda ya yi sanadin mutuwar mutane talatin da bakwai.
Bugu da kari wasu wuraren da bama-baman su ka tashi sun hada da Jisri Dayali da Hussainiyyar Rasulul-A'azam.Wannan harin na yau yana daga cikin munanan hare-haren aka kai a cikin kwanakin baya-bayan nan a yankin kamar dai yadda rahotanni suka tabbatar.
Sojojin kasar Iraki sun samu nasara hallaka mayakan kungiyar 'yan ta'addan ISIS da ke da'awar jihadi su a yau Alhamis a yankin Dayali da ke arewacin kasar, kamfanin dillancin labaran ya habarta cewa da jijjifin safiyar yau sojojin na Iraki suka kaddamar da wani farmaki a kan wata maboyar 'yan ta'addan na ISIS a wani wuri a cikin lardin Dayali, inda suka samu sa'ar hallaka tare da jikkata wasu.
Bayanin ya ce dukkanin wadanda aka kashe sun fito ne daga kasashe sha bakawai a cikin makon nan ne dai ma'aikatar harkokin wajen kasar Iraki ta sanar da cewa jagoran kungiyar 'yan ta'addan na ISIS Ibrahim Samirra'i da ke kiran kansa da suna Abubakar Bagdadi ya samu ranuka, sakamakon wasu hare-hare da jiragen yakin Iraki suka kaddamar a kan maboyarsa.
2612751