Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakaltoo daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin ta PRESS TV cewa, tun daga shekara ta 1974 dakarun kiyaye sulhu suke aiki a kan iyakokin Syria da Isra’ila wannan shi ne karon da majalisar dinkin duniya ta fitar da rahoton kan wani aikin ta’addanci da ya nuna yadda haramtacciyar kasar Isra’ila tana aikatawa a yuankin, inda raton ya nuna yadda take taimaka ma ‘yan ta’addan kasar Syria akan iyakokin kasar da suke kai hare-haren ta’addanci a kan al’ummar kasar.
A nasa bangaren a jawabinsa a yayin bude zaman Majalisar Shawarar ta Musulunci a jiya Laraba ya fayyace cewa yau fiye da shekaru uku ke nan gwamnatin amurka da wasu kawayenta suna taimaka wa ayyukan ta’addanci a kasar siriya, Sannan wasu daga cikin kasashen da suka shiga cikin sahun kawancen amurka kan yaki da ta’addanci, suna daga cikin kasashe masu goyon bayan ayyukan ta’addanci a kasar ta Siriya, kuma mafi yawan ‘yan ta’addan kasa da kasa ta cikin kasashensu suka tsallaka zuwa cikin kasar Siriya.
Ya kara da cewa shin gwamnatin amurka tana zaton wani zai gaskata da’awarta ta yaki da ta’addanci ne, alhali har yanzu tana kan bakanta na ci gaba da taimaka wa ayyukan ta’addanci, inda ko a cikin makon da ya gabata sai da ta sake gabatarwa Majalisar Dokokin kasar ta bukatar ci gaba da tallafawa wasu kungiyoyin ‘yan ta’adda a kasar siriya, wanda kuma tuni al’ummomin duniya sun gane hakan.
A lokutan bayan an samu wasu bayanai da ke tabbatar da cewa akwai dubban ‘yan ta’addan da suke kwace a asibitocin haramatacciyar kasar Isra’ila da suke karbar magani, sakamakon raunuka da suka samu a bata kashin da ake tsakaninsu da dakarun siriya, lamarin da ke kara tabbatar da cewa Isra’ila da yan ta’addan baki daya.
2616487