IQNA

Iran Ta Gabatar Da Shawarwari 10 Domin Yaki Da Ta'addanci

21:49 - December 09, 2014
Lambar Labari: 2617115
Bangaren kasa da kasa, a safiyar yau ne shugaban kasar Iran Dakta Hasan Ruhani ya bude taron kasa da kasa don fada da tsaurin ra’ayi da tashin hankali na kwanaki biyu a nan birnin Tehran don tattaunawa kan barazanar da duniya take fuskanta daga wadannan abubuwa biyu.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarat cewa, manufar wannan taro na kwanaki biyu da ya sami halartar jami’ai da masana daga kimanin kasashen 40 na duniya ita ce hada karfi waje guda tsakanin kasashen duniya don fada wannan annoba ta tsaurin ra’ayi wadda ke haifar da ayyukan ta’addanci a kasashe daban-daban na duniya.
A jawabin da ya gabatar a wajen taron shugaban kasar ta Iran Dakta Hasan Ruhani, ya bayyana tsaurin ra’ayi da tashin hankali a matsayin babbar barazanar da  take fuskantar duniya a halin yanzu don haka yayi kirayi kasashen duniya da su hada hannuwansu waje guda don fada da wannan annobar.
A watannin baya ne dai shugaban kasar ta Iran, a jawabin da ya gabatar a babban zauren majalisar dinkin duniya ya gabatar da shawarar hada karfi waje guda don fada da tsaurin ra’ayi da tashin hankali a duniya lamarin da kasashen duniya daban daban suka yi maraba da shi.
Shugaban kasar Iran Sheikh Hassan Rauhani ya kirayi kasashen yankin gabas ta tsakiya das u hada karfi da karfe domin kawo karshen ayyukan ta'addanci a yankin baki daya.

Shugaba Rauhani ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da jawabin nasa a taron kasa da kasa wanda aka bude yau a birnin Tehran kan yaki da ayyukan ta'addanci da tsatsauran ra'ayi da wuce gona da iri.

Ya ci gaba da cewa Iran ta gabatar da daftarin kudiri a majalisar dinkin duniya kan batun yaki da ta'addanci a duniya, kuma kasashen duniya suka lale marhabin da hakan, kuma hakan ya yi tasiri a sauran yankuna na duniya, in ban da yankin gabas ta tsakiya, wanda hakan ke bukatar aikin hadin gwiwa tsakanin dukkanin kasahen yankin baki daya.

Babbar manufar taron wanda ke samun halaratr wakilai daga kasashen duniya daban-daban, ita ce tattauna hanyoyin da ya kamata  abi domin magance tsatsauran ra'ayi wanda ke kai ga haddasa ta'addanci, ta hanyar wayar da kai da ilmantarwa musamman ga matasa.

2616891

Abubuwan Da Ya Shafa: iran
captcha