IQNA

Adadin Masu Karbar Addinin Muslunci A Birtaniya Ya Ninkawa

17:59 - December 14, 2014
Lambar Labari: 2618355
Bangaren kasa da kasa, wani jin ra’ayi da aka gudanar sakamakonsa ya nuna cewa adadin mutanen ad suke karbar addinin muslunci a kasar Birtaniya a cikin shekaru goma da suka gabata ya nunka

Kamfanin dilalncin labaran Iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gioz na World Bullten cewa, a cikin shekaru 10 da suka gabata fiye da mutane 5000 ne suka karbi addnin muslunci a wannan kasa da ke yammacin nahiyar turai.
Babbar cibiyar Faith matters ce ta dauki nauyin shirya wannan jin ra’ayin jama’a da kuma fitar da wannan sakamako da ke cewa cewa adadin mutanen ad suke karbar addinin muslunci a kasar Birtaniya a cikin shekaru goma da suka gabata ya nunka har sau biyu idan aka yi la’akari da yawan musulmi da kuma yadda suke karuwa.
Da dama daga cikin fiye da kashi 62 wadannan mutane ne dai sun nuna cewa sun karbi muslunci ne sakamakon binciken da suke gudanarwa wanda haka ne yaba su damar daukar kudirin karbaer musulunci, sakamakon abin da suka gano a cikinsa na koyarwa ta hakika wadda mutum dan addam ke samun kamala da ita.
Duk kuwa da cewa ana ta maganar ayyukan ta’addanci da ke bata sunan mus;nci sakamakon abin da ak shirya na bata sunan addinin ta hanyar yin amfani da wasu gurbatattun musulmin kuma bata gari, amma bayan bincike sun gane cewa addinin musulunci na zaman lafiya ba kamar yadda ‘yan ta’adda ke nunawa ba, ko kuma makiya addini.
2618052

Abubuwan Da Ya Shafa: birtaniya
captcha