IQNA

'Yan Ta'addan Daesh Na Shirin Rusa Wasu Manyan Masallatai 4 A Mausil

16:37 - December 19, 2014
Lambar Labari: 2622017
Bangaren kasa da kasa, 'yan ta'addan daesh da aka fi sani da ISIS na shirin rusa wasu manyan masallatai hudu na tarihi da ke cikin garin Mausil na arewacin kasar Iraki.

Kamfanin dilalncin labaran Iqna ya habarat cewa, ya naalto daga safin sadarwa na yanar gizo na Sautul Iraq cewa, yan ta'addan kungiyar ISIL na shirin rusa masallatai masu tarihi a garin Mausil, bayan sun yanka limamin babban masallacin birnin Mausil a arewacin kasar Iraki, bayan da yaki ya mika musu masallacin, da kuma kin bayar da fatawar korar kiristoci daga birnin. 
Wani daya daga cikin shugabannin kabilun larabawa 'yan sunna a  garin Mausil Sheikh barham ya bayyana wa tashar talabijin ta Iraqi a daren jiya cewa, 'yan ta'addan sun bukaci malamin da ya mika musu masallacin kuma ya bayar da fatawar haramcin barin kiristoci a cikin garin na Mausil, inda ya sheda musu cewa ba zai yi hakan ba, a nan take suka yanka shi.
A nasu bangaren sojojin kasar Iraki suna ci gaba da nausawa a cikin yankunan da 'yan ta'addan suka kwace iko da su, inda suke ci gaba da fatattakarsu, domin dawo da doka da oda a yankunan, da kuma dawo da dubban daruruwan mutanen da 'yan ta'addan suka kora daga yankunansu.
Wannan na daga cikin ayyukan da yan ta'addan suke aiwatrwa a kasar tare da yin kisan gilla a kan fararen hula mata da kanann yara da suke cikin wadannan yankuna a na arewacin kasar.
2620500

Abubuwan Da Ya Shafa: isis
captcha