IQNA

Kungiyar Kasashen Musulmi Ta OIC Ta Yi Maraba Da Matakin Turai Kan kafa Kasar Palastinu

16:53 - December 20, 2014
Lambar Labari: 2623531
Bangaren kasa da kasa, kungiyar kasashen muulmi ta OIC ta fitar da wani bayani dangane da yadda majalisar kungiyar tarayyar turai ta amince da daftarin kudiri na kafa kasar Pallastinu mai cin gishin kanta.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na OIC cewa, wannan kungiya ta kasashen muulmi ta fitar da wani bayani dangane da yadda majalisar kungiyar tarayyar turai ta amince da kafa kasar Pallastinu mai cin gishin kanta tare da kawo karshen mamamyar Isra'ila a cikin yankunan palastinawa.
A ci gaba da kiraye-kiraye da kuma amincewa da kafa ‘yantacciyar kasar Palastinu da kasashe da cibiyoyi daban-daban na kasa da kasa suke yi, a jiya Laraba ce dai ‘yan majalisar Tarayyar Turai suka amince da kafa kasar Palastinu mai cin gashin kanta. Majalisar tarayyar Turai din ta dauki wannan matsaya ce bayan kuri’ar da aka kada a jiya a majalisar inda ‘yan majalisar 498 suka amince da, 88 kuma suka ki sannan kuma dari da sha daya kuma suka ki kada kuri’unsu lamarin da ya sanya aka amince da wannan kudurin. 
Har ila yau a jiya Laraba ma dai, kotun tarayyar Turai din ta fitar da wani hukumci inda ta cire kungiyar Hamas mai fafutukan ‘yanto kasar Palastinun daga cikin jerin sunayen kungiyoyin ‘yan ta’adda bayan shekaru goma sha uku da sanya Hamas din cikin wadannan kungiyoyin. Kamar yadda kuma a jiyan ne dai aka tsara kwamitin tsaro zai kada kuri’a kan wani kuduri da aka gabatar masa dangane da ayyana lokacin da Isra'ila za ta kawo karshen mamayar da take yi wa yankunan Palastinawa da aka tsara a shekarar alif dari tara da sattin da shida.
2623247

Abubuwan Da Ya Shafa: oic
captcha