IQNA

An Kafa Cibiyar Bunkasa Harkokin Kur’ani Ta Babban Masallacin Azhar

16:53 - December 22, 2014
Lambar Labari: 2625015
Bangaren kasa da kasa, an bude wata babbar cibiya wadda za ta kula harkokin kur’ani mai tsarki karkashin kulawar kwamitin babban masallacin juma’a na jami’ar Azahar a kasar Masar.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar yaum sabi cewa, a cikin wannan mako an bude wata babbar cibiya wadda za ta kula harkokin kur’ani mai tsarki karkashin kulawar kwamitin babban masallacin juma’a na jami’ar Azahar a da ke birnin kahira na kasar Masar da nufin samar da wani yanayi na kula da ayyukan kr’ani zalla.
Daga cikin muhimamn ayyukan da wannan bangare na kur’ani zai rika aiwatarwa, akwai shirya bayar da horo ga matasa da suke da sha’awar koyon kira ta kur’ani mai tsarki, kamar yadda za a samar da tsari na harda da kuma koyar da ilimin tajwidi na kyautata karatun kur’ani, wanda zai taimaka matuka wajen samar da sabbin makaranta da mahardata a tsakanin matasan da za su samu horon.
Haka nan kuma wasu daga cikin fitattun malamai da makaranta kur’ani na kasar sun bayar da cikaken goyon baynsu ga wannan da kuma yadda za a aiwatar da shi, inda suka bayyana shirinsu na bayar da dukkanin gudunmawa da taimakonsu domun tabbatar da cewa ya yi nasart kamar dai yadda aka shirya.
Masar tana daya daga cikin kasashen musumi da suke bayar da muhimmanci matuka wajen karatun kur’ani mai tsarki da hakan ya hada da shiga gasarsa a matsayi na duniya.
2624707

Abubuwan Da Ya Shafa: azhar
captcha