IQNA

Ana Horar Da Limaman Faransa A Moroco Kan Yaki Da Tsatsauran Ra’ayi

15:07 - December 23, 2014
Lambar Labari: 2625116
Bangaren kasa da kasa, Limamai 50 ne daga kasar Faransa suke samun horo a kasar Moroco domin yaki da mummunar akidar tsatsauran ra’ayi da kafirta musulmi da ke mayar da matasa ‘yan ta’adda.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Morocco World News cewa, a cikin wannan mako ne aka fara gudanar da wani shiri na horar da malaman addinin da ke limanci a kasar Faransa dangane da sani yadda za su bullowa matasa da ke ake rudawa tare da saka musu akidar kafirta musulmi da ta’addanci.
Wannan horo dai ya hada da koyar da su hakikanin sanin manonin ayoyin kur’ani mai tsarki da kuma sirar manzon Allah (SAW) da kuma sauran batutuwa da ya kamata su samu masaniya a kansu kamar dai yadda bayanin ya yi ishara.
Adadin matasa da ke tafiya zuwa ta’addanci tare da hadewa da kungiyar Daesh daga kasar Faransa yana karuwa, a kan hakan ne mahukuntan kasashen biyu suka shirya wannan horo domin samun mafita.
2624965

Abubuwan Da Ya Shafa: morocco
captcha