IQNA

Babban Taron Mabiya Addinin Muslunci A Arewacin Kasar Amurka

15:17 - December 23, 2014
Lambar Labari: 2625119
Bangaren kasa da kasa, an gudanar da babban taron mabiya addinin muslunci na arewacin Amurka a birnin Tronto na kasar Canada a wannan mako.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na On Islam cewa, a cikin wannan mako an gudanar da babban taron mabiya addinin muslunci na arewacin Amurka a birnin Tronto na kasar Canada domin tattauna batutuwa da suka shafe su.
Bayanin ya ci gaba da cewa ko shakka babu musulmin kasar suna mayar da hankali matuka wajen tattauna lamurra da suka shafe su da kuma wadanda ska shafi duniyar musulmi, musamman ma  acikin wannan yanayi da ake kara samun bullar wasu kungiyoyi masu tsatsauran ra’ayi da ke kara tsananin adawa ga msuulmi mazauna wadannan kasashe.
An fara gudanar da wannan taro ne a cikin shekara ta 2003 domin kalu balantar abin da ake yadawa dangane da addinin musulunci bayan harin 11 ga September na ta’addanci, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama .
Musulmi dai dais u ne suka fi saurin karuwa  akasar Canada inda a halin yanzu su ne kashi 3% na dukkanin al’ummar kasar.
2624839

Abubuwan Da Ya Shafa: canada
captcha