Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Anadolu Agency cewa, jam’iyyar Green Party masu tsananin adawa daga cikin ‘yan majalisar dokokin kasar Jamus daga sun gaegadin cewa idan ba adauki mataki ba dangane da kara yaduwar musulmi a kasar nan da wani lokaci mai zuwa musulmi zasu mayar da kasar Jamus kasar muuslmi.
Bayanin ya ci gaba da cewa mutanen kasar Jamus kimani dubu sha biyar ne suka gudanar da zanga zangar yin Allah wadai da yadda gwamnatin kasar take karban baki musamman daga kasashen musulmi tare da nuna rashin amincewa da hakan.
A cikin yan lokutan na wata sabuwar kungiya mai suna turawa masu kishin kasa da kuma nuna rashin amincewa da musuluntar da kasarsu ta gudanar da zanga zanga ta lumana a gabacin kasar ta Jamus a jiya litinin, wanda ya kafa kungiyar tun watan oktoban da ya gabata ya ce jama’a na tare da su, kuma yawansu na karuwa ta yadda yan siyasar kasar basu isa su yi watsi da su ba a cikin kasar.
Babban ministan sharia na kasar ya ce zanga zangar wani “abin kunya ne ga kasar Jamus wacce ta zama budaddiyar kasa ga baki, kafin haka dai, waziriyar kasar Angela Merkel ta ja kunnen mutanen kasar kan ayyukan kungiyar ta.
Wanda yake shin shugaban musulmi na kasar ta Jamus Aiman Mazyek, ya ce akwai tsoron cewa kungiyar, zata raba kan jamusawa tsakanin musulmi baki da kuma yan asalin kasar ta Jamus, kungiyar na mabiya dubu ashirin da biyu.
Amma dai mutane dubu goma ne suka shiga zanga-zagar, banda Amurka kasar Jamus ce kasar da ta fi karban baki daga kasashen duniya musamman daga kasashen musulmi, sannan itace ta fi karfin tattalin arziki a nahiyar baki daya.