
Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Al-wifagh cewa, Jami’an tsaron kasar Bahrain sun kame shugaban kungiyar hamayya mafi girma ta kasar Sheikh Ali Salam. A wani bayani da kungiyar al-wifaq ta kasar Bahrain ta fitar a yau asabar tabbatar da kame shugaban nata bayan da sashen binciken manyan laifuka na ‘yan sandan kasar ya gayyace shi, sannan kuma da mika shi zuwa ga ma’aikatar sharia.

Da safiyar yau asabar ne dai sashen binciken manyan laifuka da ke karkashin ma’aikatar cikin gida ya gayyaci Sheikh Ali Salman domin yi masa tambayoyi da misalin karfe biyu na rana. Tun mutane su ka fara yin cincirindo a kofar gidan shugaban kungiyar ta al-wifaq domin nuna kin amincewarsu da kamun da aka yi masa.
Tun a shekara ta dubu biyu da sha sha daya ne Al’ummar Bahrain su ka fara yunkurawa domin samar da sauye-sauye ta fuskar siyasa a cikin kasar, sai dai a lokuta da dama mahukuntar kasar sun yi amfani da karfi domin murkushe su.
Su ma a nasu bangaren malaman addinin muslunci a kasar Bahrain sun yi kakkausar suka da yin Allawadai da tsare Sheikh Ali Salman shugaban jam’iyyar Al-wifagh da aka yi a cikin kwanakin nan.
A nasu bangaren kungiyoyin kare hakkin bil adama na kasa da kasa sun kwatanta gidajen kason kasar Bahrain da gidajen kason gwamnatin 'yan tsatsauran ra’ayi na kasar Jamus karkashin jagorancin shugabansu hitla.

A cikin wani bayani da wasu daga cikin kungiyoyin kare hakkin bil adama suka fitar jiya daga wata babbar cibiyarsu da ke birnin London na kasar Birtaniya, sun bayyana irin matakan da mahukunatan kasar Bahrain suke dauke a cikin gidajen kaso wajen azabtar da 'yan adawar siyasa da cewa ya wuce haddi na 'yan adamtaka.
Bayanin ya kara da cewa masarautar Bahrain tana azabtar da 'yan adawar siyasa a gidajen kaso da hakan kan kai su ga rasa rayukansu ko wasu bangarorin jikinsu, inda ake yin amfani da duk wani salon a azabtarwa da a kan masu adawa da salon siyasar gidan sarautar kasar.
Kungiyoyin suka ce masarautar Bahrain ta hana kungiyoyin kare hakkin bil adama na kasa da kasa su ziyarci mutanen da ake tsare da su a kasar, tare da hana ganawa da mutanen da suka rasa danginsu sakamakon ukubar da masauratar ta Bahrain ta gana musu a gidajen kaso.
2645737