Kamfanin dillancin labaran iqna ya ahbarat cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Sadal Balad cewa, a jiya ne babbar cibiyar mulunci a kasar Masar ta Azhar ta fitar da wani bayani da wanda ya yi kakkausar da yin Allawadai da kai harin da wasu masu tsatsauran ra’ayin kin muslunci suka yi kan wani masallaci a kasar Sweden a cikin wannan mako da muke ciki.
Bayanin ya ci gaba da cewa wasu daga cikin masu tsananin adawa da addinin mulsunci suna aikata ta’addanci kan musulmi a cikin kasashen turai ba tare da daukar matakan ladabtarwa daga gwamnatocin wadanann kasashen ba, tare da bayyana abin da suke aikatawa da cewa fadin albarkacin baki ne ko kuma yanci ne dna dan kasa, ba tare da yin lakari da munin da ke tattare da wannan aiki ba.
Masu adawa da musulmi a kasar Sweden dai sun jima suna gudanar da aikace-aikacensu a kasar, inda suka shahara da nuna tsananin kiyayya ga duk wani abu da ya danganci addnin musulunci ko kuma musulmi, musamman ma a halin yanzu da waus ke aikata ta’addanci da sunan musulunci.
Da dama daga cikin kungiyoyin kare hakkin bil adama a kasashen turai da na musulmi sun tir da wannan aiki, tare da neman da a gurfanar da duk wadanda suke da hannua acikin lamarina gaban kuliya dokin su fuskanci hukunci.
2658864