Kamfanin dilalncin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na World Bulletin cewa yanzu haka sns gudanar da taron maulidin manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan gidansa tsarkaka a masallatan kasar Turkiya abirane da daman a kasar.
Bisa ruwaya ta wasu bangaren musulmi ranar sha biyu ga wata Rabi’ul Awwal shi ne ranar haihuwar manzo, wanda bisa hakan a jiya Laraba mabiya addinin muslunci a birnin kasar sun gudanar da taron maulidin manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan gidansa kamar dai yadda aka saba gudanarwa a wasu biranan kasar da dama.
Kasar Turkiya dai na daga cikin kasashe da ke yawan musulmi kasantuwar kasar tana da alaka da kasashen larabawa musamman daga kassahen larabawan da ke yankin gabas ta tsakiya da ma wasu daga yankin arewacin nahiyar Afirka, wadanda wasu daga cikinsu suna zaune a kasar yayin da wasu kuma ske da alaka da kasar ta wasu hanyoyi.
Gudanar da tarukan maulidin manzon Allah a wannan birnin a wannan karo wata manuniya ce dangane da irin ci gaban da musulmi suke samu a kasar, da kuma yadda wannan addini yake ci gaba da kara yuwaduwa da bazuwa wasu yankuna na kasa.
2670552