Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, a lokacin da yake gabatar da jawabinsa a gaban taron makon hadin kai, Haiel Abdolhafiz Dawud minisan mai kula da harkokin addini a kasar Jordan ya bayyana cewa kasashen yammacin turai suna iyakacin kokarinsu domin tabbatar da sun rarraba kan al’ummar musulmi ko ta wane hali suka samu damar yin hakan.
Tun da safiyar yau ne dai aka bude wannan taro na hadin kan al’ummar musulmi a nan birnin tehran wanda zai dauki kwanaki uku ana yinsa, wanda kuma ya sami halartar malamai da masana daga kimanin kasashe hamsin na musulmi inda suke gabatar da jawabai da kuma makaloli na hadin kai.
Ministan ya bayyana hakan ne yau a lokacin da yake halartar taron makon hadin kai a babban birnin jamhuriyar muslunci, inda ya ci gaba da cewa lokaci ne al’ummar musulmi suna rayuwa cikin wani irin yanayi na daban wanda ke bukatar su zama cikin fadaka domin fayyace hakikain abin da ake kulla musu domin rarraba su da sunan addini ko banbancin mazhabobi da sauransu, wanda kuma hakan yana bukatar da yin taka tsantsan matuka wajen daukar mataki domin fuskantar wannan babbar barazana.
Haiel Abdolhafiz Dawud ya ci gaba da cewa a halin da ake cikin yanzu dole ne sai musulmi na duniya sun hada kansu ne za su iya gano makircin da makiyansu suke kulla musu domin rarraba kansu, kuma rashin hakan zai zama ya bude wata kafa da makiya muslunci za su yi amfani da ita domin ci gaba da kara fadada barakar da ke tsakanin mabiya addinin muslunci a duniya baki daya.
A kowace shekara dai ana gudanar da wannan taro wanda kuma ko shakka babu yana yin matukar tasiri wajen kara wayar wa musulmi da kansu dangane da abin da ake kulla musu a duniya yammaci.
2683092