Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Al-bawwabah News cewa mai baiwa babban malamin cibiyar Azhar shawara kan harkokin zamantakewa Mohammad Mahna ya bayyana cewa taya mabiya addinin kirista murna kan zagayowar haihiwar annabi Isa (AS) hakan wata manuniya ce kan kyakyawar mu’amala da ke tsakanin bangarorin biyu.
Ya ci gaba da cewa Allah madaukin sarki ne ya fara ambaton hakan a cikin kur’ani mai tsarki dangane da haihiwar annabi Isa Almasih (AS) inda yake bayyana abin da annabi Isa yake fada tun yana jinjiri cewa, amincin Allah ya tabbata a gare ni a ranar da aka haife ni, da kuma ranar da zan rasu da ranar da za a tayar da ni rayayye.
Dangane da ziyarar da Sheikh Ahmad tayyib ya kai majami’ar Kibtawa kuwa, Mahna ya ce hakan ya kara tabbatar wa mabiya addinin kirista cewa musulmi ba makiyansu ba ne, kuma hakan ya kara dankon zumunci tsakanin musulmin kasar Masar da kuma mabiya addinin kirista na kasar, wanda kuma hakan shi ne koyarwar addinin musulunci.
2677766