Kamfanin dilalncin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daha shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Al-watan cewa Iyad Amin Madani babban sakataren kungiyar kasashen musulmi ta OIC ta sheda cewa sun fara tatatuna batun shigar da karar jaridar Charlie Hebdo saboda saka hotunan zanen batunci ga manzon Allah (SAW) a makon da ya gabata.
Kungiyar ta yi kakkausar suka dangane da sake yada zanen batuncin nan da jaridar Lomond ta yi ga manzon Allah (SAW) a kasar ta Faransa a yau duk kuwa da irin nuna bacin rai da musulmi suka nuna dangane da abin da jaridar take yi a cikin lokutanan.
Haka nan ita ma anata bangaren gwamnatin Jamhuriyar Musulunci ta yi Allah wadai da sake buga hoton zane na batanci ga masulunci wanda jiridar nan ta Charlie Hebdo ta kasar faransa ta yi, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar ce ta yi wannan wadai ta kuma kara da cewa yin zanin mai batanci ga musulmi fiye da billion guda a duk fadin duniya abune wanda bai dace.
Kuma hakan ba abinda zai kawo in banda kara ingiza ayyukan ta’addanci a duniya, hakan nan cibiyar muslunci a masar ma ta fitar da irin wannan sanarwan inda yay i suka dangane da sake buga wannan zanen, sannan ta bayyana cewa hakan ba abinda zai haifar sai karin tashe tashen hankula a cikin mutane da dama.
2721511