amfanin dilalncin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na jaridar Guardian cewa, Shoja Shafi shugaban majalisar musulmin kasar Birtaniya, ya shirya wani zaman taro na shugabannin musulmin kasar, domin tattauna dangane da hanyoyin da za a bi wajen tunkarar masu tsatsauran raayi da ke bata sunan addinin muslunci a kasar da ma a idon duniya, musamman a turai.
A bangare guda kuma wata cibiyar musulmi ta dauki nauyin shirya wannan jin ra’ayin jama’a da kuma fitar da wannan sakamako da ke cewa cewa adadin mutanen ad suke karbar addinin muslunci a kasar Birtaniya a cikin shekaru goma da suka gabata ya nunka har sau biyu kamar yadda aka bayyana a cikin bayanin.
Bayanai sun ce fiye da kashi sittin wadannan mutane ne dai sun nuna cewa sun karbi muslunci ne sakamakon binciken da suke gudanarwa wanda haka ne yaba su damar daukar kudirin karbaer musulunci, sakamakon abin da suka gano a cikinsa na koyarwa ta hakika wadda mutum dan addam ke samun kamala da ita a cikin rayuwarsa mai ma’ana.
Wanann dai ya zo ne duk kuwa da cewa ana ta maganar ayyukan bata gari da ke bata sunan mus;nci sakamakon abin da ak shirya na bata sunan addinin ta hanyar yin amfani da wasu gurbatattun musulmin kuma bata gari da kuma jahilai na addini.
Kasar Birtaniya na daga cikin kasashen turai da ke da yawan musulmi wadanda suke samun karuwa ta fuskar adadi a kowace rana, duk kuwa da cewa akwai kaidoji na fitar hankalia da akan ginaya musu a wasu lokutan.
2722578