Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na tashar Almanar cewa, Shekh Muhammad Mauid kakakin babbar majalisar malaman gwagwarmayar muslunci ta Palastinawa mazauna Lebanon ya ce gwagwarmaya za ta mayar da martani da ya dace kan haramtacciyar kasar Isra’ila kan kisan ‘yan kungiyar Hizbullah da ta yi a jiya a cikin yanku Kunaitara na Syria.
Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta HIzbullah a kasar Lebanon ta sanar da shahadar mayakanta da dama a yau lahadi, a wata sanarwar da kungiyar ta Hizbullah ta fitar a yau lahadi ta ce da dama daga cikin ‘yan gwgawarmaya sun yi shahada a sanadin wani harin da jirgin yankin ‘yan sahayoniya ya kai a yankin Qunaidharan da ke kan iyakokin Lebanon da Syria.
Majiyar sojan Syria ta ce wani jirgi mai saukar angulu na ‘yan sahayoniya ne ya harba makami mai linzami a yankin na Qunaidharah. Kungiyar gwagwarmayar ta Hizbullah ta ce nan gaba kadan za ta sanar da sunayen wadanda su ka yi shahadar. Sai dai wasu kafafen watsa labaru sun ce daga cikin wadanda su ka yi shahadar da akwai dan jawad mugniyah.
2728110