Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Ina cewa, a jiya Laraba a wani zaman taron manema labarai ma’aikatar harkokin wajen Palastinawa ta yi Allawadai da kakkausar suka dangan da yadda yahudawan sahyuniya suke shishiga kan masallacin quds.
Wasu tsagerun yahudawan sahayoniyya sun kai farmaki gonakin Palasdinawa tare da karya bishiyoyin zaitun a gabar yammacin kogin jodan, kafofin watsa labaran Palasdinawa sun bayyana cewar a farmakin da tsagerun yahudawan sahayoniyya suka kai kan gonakin Palasdinawa a yankin Yada da ke kudancin garin alil a gabar yammacin kogin sun karya tarin bishiyoyi
A halin yanzu haka dai al’ummar kudancin garin na Khalil suka karkashin kawanyar sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila kuma suna fama da matsalolin karacin kayayyakin more rayuwa musamman ruwa da hasken wutan lantarki.
Kungiyar gwagwarmaya mai muliki ta dora alhakin harin da wani matasin Palastinu ya kai kan wasu yahuwa a babban birnin yahudawan, kamfanin dillancin labarai na Kudus ya nakalto babban saktaren kungiyar Majalisar juyin juya hali na fatah na cewa mumunan siyasar Gwamnatin haramtacciyar kasar Israila ta kame-kame,ci gaba da mamaye kasar Palastinu, kai hari kan Masallacin Kudus mai tsarki tare da ci gaba da kisan fararen hula shine ya tilastawa matasan Palastinu kan irin wannan hari.
2739913