IQNA

Mabiya Addinai A Kasar Portugal Sun Addu’ar Zaman lafiya

21:41 - January 26, 2015
Lambar Labari: 2767849
Bangaren kasa da kasa, mabiya addinan muslunci da Kiristanci da kuma yahudanci sun hadu a babban masallacin birnin Lisbon fadar mulkin kasar Portugal domin yin addu’ar sulhu da zaman lafiya.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na ATLASINFO.FR cewa, bangarorin da suka taru sun ajiye a kan cewa za a gudanar da wasu tarukan makamantan wannan a majami’oin Ranto da kuma Santo Antonio dake cikin birnin Lisbon, tare da halartar dukkanin bangarorin addinan da suka taru a masallacin.
Khoze Aulman babban jagoran mabiya addinin yahudanci a kasar ta Portugal ya bayyana cewa wadannan addinai guda uku suna da abubuwan da suka hada su, wadanda sun fi abubuwan da suka raba su yawa, a kan haka dole ne su raya su domin samun fahimtar juna da zaman lafiya tare a tsakanin dukkanin mabiya wadannan addinai.
Shi ma a nasa bangaren jagoran mabiya addinin kirista na darikar Katholika ya bayyana cewa wanna taro yan ada matukar muhimmanci, kuma majami’arsa za ta dauki nauyin shirya taro nag aba domin haduwa a tsakanin mabiya addinai na sama domin yin addu’a ta zaman lafiya da sulhu a tsakaninsu.
A nasu bangaren mabiya addinin Hundus sun gudanar da nasu tarukan da addu’oin a wani babban daki da suke yin harkokin ibadarsu, inda a can ma suka yi addu’a bayan kai harin birnin Paris.
2763346

Abubuwan Da Ya Shafa: portugal
captcha