IQNA

Musulmin Canada Na Wayar Da Kan Jama’a Dangane Da Musulunci

12:43 - January 29, 2015
Lambar Labari: 2778863
Bangaren kasa da kasa, kungiyar musulmin Calgary ta shirya wani zama domin wayar da kan wadanda ba musulmi dangane da yadda suke kallon addinin muslunci.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Radio Canada cewa, babbar manufar shirya wannan zama dai ita ce wayar da kan wadanda ba musulmi dangane da yadda suke kallon addinin muslunci musamman ma dai bayan abubuwan da suka faru a cikin lokutan nan a kasar faransa.
An shirya zaman taron ne  ababban masallacin birnin Calgary da ke arewacin kasar ta Canada, wanda kuma hakan yay i tasiri matuka wajen kara bayyana hakikanin abin da yake faruwa da kuma yadda ake kokarin yin amfani da hakan a siyasance domin bata sunan addinin muslunci a duniya musamman ma daia  cikin kasashen yammacin turai.
A cikin makon da ya gabata ne wata mata musulma ta fuskanci batunci da cin zarafi a birnin na Calgary, daga wani mutum wanda ba musulmi ba, amma daga bisani an tilasta neman uzuri daga gare ta.
2774710

Abubuwan Da Ya Shafa: canada
captcha