Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Almisriyun cewa, Muhamad Gormez a wani zaman da aka gudanar a dakin taruka na birnin Ankara ya sheda cewa ya zama wajibi a aike da sakon sulhu zuwa ga dukkanin jagororin addinai na duniya domin samun fahimta da kuma kawar gaba.
A cikin makon da ya gabata ne jagoran juyin Islama ya rubuta sako na musamman ga matasan kasashen yamma da na arewacin Amurka, yana kiransu da su yi nazari cikin addinin Musulunci, nazari wanda ya bambanta da wanda shuwagabannin siyasara kasashensu suke nuna masu.
Don su gane Musulunci na asali na kuma gaskiya, jagoran ya yi nuni da cewa a cikin shekaru ashirin da suka gabata kasashen yamma sun yi kokarin nunawa duniya musamman matasansu cewa wannan addini mai girma abin tsoro ne, kuma shi ne makiyinsu, wanda yakamata su ji tsoronsa.
A gaskiya nuna kiyayya ga addinin Musulunci da kuma nisanta mutane daga gareshi ba wani sabon abu bane a tarihin siyasar turawan yamma da Amurka.
Banda haka, kasashen yamma da Amurka suna da mummunan tarihi na bautar da mutane, musamman wadanda ba kiristoci ba a duk fadin duniya, sannan ga bakar mulkin mallaka da suka yiwa kasashen duniya da dama, wanda ya hada da nuna wariyar launin fata, ko kuma fifita kibilarsu kan sauran kabilu a cikin karnuka da suka shude.
Har’ila yau jagoran ya yi kira ga matasan da su yi dubi a cikin littafan da masu binciken tarihin kasashen yamma da Amurka suka rubuta kan yakokin mazhabobin kiristoci, da kuma zubar da jini kan kabilanci ko yankasanci wadanda suka jawo yakokin duniya na daya nan a biyu., inda miliyoyin mutanen yankin turai da Amurka suka rasa rayukansu mummunanr siyasar shuwagabannin wadannan yankunan.
A cikin sakon jagoran juyin juya halin Musulunci ya yi kira da matasan kasashen yamma da Amurka da su tambayi masu bincike da masanansu kan dalilin da ya say an siyasarsu ke katangance su kan irin sauye sauyen da ke faruwa a duniyar mu ta yau, wanda ya shafi addinin Musulunci, me yasa yan siyasar wadannan kasashe suke fada da yaduwar al-adun Musulunci a cikin kasashen turai da Amurka.
Gaskiyan lamarin shi ne irin sakonnin da halayen da addinin Musulunci yake da su, wadanda suka yi karo da manufofin shuwagabannin kasashen yamma na ci gaba da dora kansu kan mutane a duk fadin duniya, na daga cikin dalilan da suka sanyasu samar da tsoron addinin Musulunci cikin matasan kasashen su.
A wani bangaren katangance matasan kasashen yamma daga abubuwan da suka shafi kamun kai da kyatanta halaye na gari, wadanda addinai suka zo da su, hakan zai kaisu ga lalacewa ne cikin dabi’u da halaye na halaka.
2774748