IQNA

Kungiyar Kasashen Musulmi Ta Yi Allawadai Da Ta’addancin daesh

16:54 - February 04, 2015
Lambar Labari: 2809492
Bangaren kasa da kasa, kungiyar kasashen musulmi ta yi kakakusar suka dangane da kisan rashin imani da kungiyar yan ta’adda ta yi wa sojan kasar Jordan Mu’az Kasasibah.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na OIC cewa, kungiyar ta yi kakakusar suka dangane da kisan rashin imani da kungiyar yan ta’adda ta yi wa sojan kasar Jordan Mu’az Kasasibah ta hanyar kone shi da wuta.
Ita ma a nata bangaren g wamnatin kasar Jordan ta sanar da cewa ta aiwatar da hukuncin kisa kan masu tada kayar baya guda biyu da ake tsare da su, hakan dai wani martani ne ga kisan da mayakan IS suka yi wa matukin jirgi dan kasarta.
Daya daga cikinsu mai suna rishawi 'yar kunar bakin wake ce, wadda IS suka bukaci ayi musayar ta da matukin jirgin da suke tsare da shi, gwamnatin Jordan ta sha alwashin daukar fansa akan kisan da mayakan IS suka yi Mu'az al-Kasesbeh a wani hoton bidiyo mai daga hankali da aka nuna yadda suka banka masa wuta alhalin yana raye.
Daruruwan mutane ne suka fito akan titunan babban birnin kasar Aman, su na bukatar a dauki fansa kan kisan da aka yi wa laftanal-kanal Mua'az al-Kasasbeh. Kuma mahaifinsa na daga cikin wadanda sukai wannan machi, sai dai gwamnatin Jordan ta ce jinin sa ba zai tafi a banza ba.
An yankewa AL-Rishawi hukuncin kisa a shekarar dubu biyu da biyar saboda rawar da ta taka a harin kunar bakin wake da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane sittin, shi ma wani babban jigo na kungiyar al-Qaeda Ziyad Karbili da ya kashe wani dan asalin Jordan an kashe shi a yau.
2809407

Abubuwan Da Ya Shafa: oic
captcha