
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa a yanar gizo na jaridar Al-tahrir cewa, a cikin wani bayani da ya fitar a jiya Ahmad Tayyib babban malamin cibiyar Azhar ya bayyana cewa ‘yan ta’addan daesh ba su da wata alaka da addinai da aka safkar daga sama saboda haka ya halitta a halaka su a duk inda aka same su.
Babban malamin na jami’ar Azhar ta kasar Masar ya zargi wasu kasashen yammacin Turai da na Larabawa da hannu a goyon bayan ayyukan ta’addanci a kasar ta Masar da ma sauran kasashen musulmi.
A jawabinsa a yau babban ya bayyana cewar wasu kasashen yamma da ‘yan koransu na kasashen Larabawa ne suka cunawa kasar Masar ‘yan ta’adda kuma da kudaden irin wadannan kasashe kungiyoyin ‘yan ta’adda suke ci gaba da aiwatar da munanan ayyukansu na kashe-kashen rayuka da barnata dunkiyar al’umma.
Shhin malamin ya kara da cewar maha’inta da shaidan ya hurewa kunne suke daukan nauyin ayyukan ta’addanci a Masar. A hare-haren ta’addancin baya bayan nan da aka kai kasar ta Masar sun yi sanadiyyar mutuwan jami’an tsaron kasar da fararen hula kimanin talatin tare da jikkatan wasu da dama a yankin Sina. A bayan kai hare-haren shugaban kasar Masar ya bada umurnin kafa wata runduna da zata dauki alhakin yaki da ta’addanci a kasar.
Ana ci gaba da yin Allawadai da wanann aiki na ta’addanci da kungiyar ta Daesh ta aikata kan matukin jirgin sama na kasar Jordan ta hanyar kona shi da wuta kurmus.
2808398