Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Press TV cewa, yanzu haka Netanyahu kamar yadda jaridar Daily Mail ta kasar Birtaniya ta ruwaito yana shirin rusa gidajen palastinawa.
Yanzu haka ana ci gaba da kiraye-kiraye da kuma amincewa da kafa ‘yantacciyar kasar Palastinu da kasashe da cibiyoyi daban-daban na kasa da kasa suke yi, a jiya Laraba ce dai ‘yan majalisar Tarayyar Turai suka amince da kafa kasar Palastinu mai cin gashin kanta.
Majalisar tarayyar Turai din ta dauki wannan matsaya ce bayan kuri’ar da aka kada a jiya a majalisar inda ‘yan majalisar dari hudu casein da takwas suka amince da, tamanin da takwas kuma suka ki sannan kuma dari das ha daya kuma suka ki kada kuri’unsu lamarin da ya sanya aka amince da wannan kudurin.
Har ila yau a jiya Laraba ma dai, kotun tarayyar Turai din ta fitar da wani hukumci inda ta cire kungiyar gwagwarmaya mai fafutukan ‘yanto kasar Palastinun daga cikin jerin sunayen kungiyoyin ‘yan ta’adda bayan shekaru goma sha uku da sanya ta din cikin wadannan kungiyoyin.
Kamar yadda kuma a jiyan ne dai aka tsara kwamitin tsaron zai kada kuri’a kan wani kuduri da aka gabatar masa dangane da ayyana lokacin da za ta kawo karshen mamayar da take yi wa yankunan Palastinawa da aka tsara.
2819092