Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Al-tahrir cewa, daya daga cikin mahalartan gasar 20 ya bayyana cewa tun a farkon wannan mako ne a fara wannan gudanar da wannan gasa ta karatun kur’ani mai tsarki.
Wasu daga cikin malaman kur’ani na kasar kamar su Muhammad Bashar da kuma Muhammad Abul Asrar sun samu halartar gasar domin duba irin ci gaban da daliban jami’oi suke samu ta fuskar karatu da kuma hardar kur’ani mai tsarki a kasar, wanda hakan zai zama wata alama ce da ke nuna irin ci gaban da ake samu ta wanna fuska a kasar.
A karshen wannan mako ne dai za a kamma gasar, tare da bayar da kyautuka ga wadanda nuna kwazo a dukkanin bangarorin da aka gudanar da gasar, bugu da kari kuma ana bayar da horo ga matan kan wasu ilmomi na addinin a gefen taron wannan gasa ta kur’ani.
2832720