Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya habarta cewa a zantawar day a yi da Yahya Muhammad daya daga cikin yan kungiyar Ansarullah a kasar Yeman ya bayyana cewa, sun samu tunaninsu ne na neman yanci daga rayuwar Imam Khomenini (RA) yardarm Allah ta tabbata a gare shi.
A nasa bangaren jagoran juyin Islama a cikin jawabin da ya yi a ganawarsa da wasu kwamandojin sojin saman kasar jagoran ya jaddada cewa al'ummar Iran suna nan daram a kan bakansu na bin tsarin jamhuriyar Islama, kuma a wannan karon ma za su baiwa maras da kunya kamar yadda suka saba a cikin shekaru talatin da shida da suka gabata a duk lokacin da a ke gudanar da bukukuwan zagayowar ranakun nasarar juyin juya a kasar.
Baya ga hakan kuma, wani abu da ya dauki hankula matuka a cikin jawabin na jagora shi ne, yadda ya caccaki Amurka dangane da irin gabar da take nuna wa kasar ta Iran a cikin wadannan shekaru , da kuma yadda take ta kokarin ganin ta mayar da Iran saniyar ware a cikin dukkanin harkoki na ilimi da ci gaba da kuma siyasar duniya, lamarin da ya tabbatar da cewa Amurka ba ta yi nasara a kansa ba.
Dangane da batun tattaunawar da ke gudana tsakanin Iran da manyan kasashen duniya kan shirinta na nukiliya kuwa, jagoran ya bayyana cewa ba su da matsala kan cimma yarjejeniya kan hakan, matukar dai yarjejeniyar za ta girmama tare da mutunta manufofin jamhuriyar musulunci, ya ce amma ga dukaknin alamu daya bangaren ba a shirye yake domin yin hakan ba, ya kara da cewa da Iran ta amince da mummunar yarjejeniya, gara a ce ba a cimma wata yarjejeniya ba.
2832734