IQNA

An Gudanar Da Zanga-Zangar Kin Jinin Boko Haram A Jamhuriyar Nijar

20:57 - February 18, 2015
Lambar Labari: 2868436
Bangaren kasa da kasa, Al’ummar Jamhuriyyar Nijar sun gudanarda gangamin nuna adawa da kungiyar Boko Haram data soma kai hare-hare a kasar tare da nuna goyan bayansu ga jami’an tsaron kasar da suka shiga yaki da tsagerun kungiyar.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Al-shuruq cewa, kawancen jam’iyyun da ke kan karagar mulkin Jamhuriyar Nijar ya bukaci al’ummar kasar baki daya da su gudanar da zanga-zangar nuna goyon baya ga gwamnatin kasar wadda ta kuduri aniyyar fada da mayakan Boko Haram da suka soma kai wa kasar hare-hare.
Jam’iyyun siyasar sun bukaci a gudanar da wannan zanga-zanga a ranar 17 ga wannan wata na Fabarairu a duk fadin kasar.
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da shugaban kasar Mahamadou Issifou ya bukaci al’ummar kasar da su mara wa sojoji da kuma sauran jami’an tsaron kasar baya a kokarin da suke na kare iyakokin kasar daga barazanar wannan kungiya.
A cikin yan lokutan nan mayakan na Boko Haram sun kaddamar da hare-hare a cikin yankuna na kasar ta Nijar, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama.

2865171

Abubuwan Da Ya Shafa: Niger
captcha