Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na The Eagle cewa, dalibai musulmia jami'ar Texas ta kasar Amurka sun gudanar da wani zama na wayar da kai ga sauran dalibai wadanda ba musulmi ba dangane da addinin muslunci da kuma koyarwarsa.
Wannan shiri dai ana gudanar da shi ne a kowane wata, kuma akan gayyacio malami dam asana domin gabat da laccoci ga daliban, lamarin da yak esamun tasiri matuka a takanin daliban, a cikin watan day a gabata ne dai wasu mutane dab a a san ko su wane ne ba suka bnaka wuta aan babbar cibiyar musulmi ta birnin na Texas.
Tun kafin wannan lokacin dai mutanen da suke da tsananin kiyayya da musulmia jahar sun nuna adawarsu da duk wani shiri na msuulmi na taro da abin day a yi kama da hakan, inda suke bukatar mahukunta a kasar da su hana musulmi gudanar da harkokinsu.
Addininn muslunci yana mabiya fiye da bilyan damiliyan 600 a duniya, kuma shi ne addinin da yafi kowane addini a duniya saurin samun karbuwa a wajn sauran al'ummomi mabiya wasu addinai, kamar dai yadda bincike ya tabbatar da hakan.
Abubuwan da suke faruwa na ta'addanci da sunan addinin muslunci da wasu ke aiakatawa ya yi tasiri a tsakanin wasu mabiya awasu addinai wajen bata sunan addinin muslunci a idon duniya, wanda kuma musulmi bas u amince da hakan, domin yan taadda bas u wakiltar musulmi.
2882522