Kamfanin dilalncin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Huffington post cewa, Creeg Maco shugaban cibiyar kula da harkokin msuulmi a kasar ta Amurka ya bayyana cewa, a wani jin ra’ayin jama’ar Amurka da suka gudanar sakamakon jin ra’ayin ya nuna cewa da dama daga cikin Amurkawa na ganin musulmi a matsayin mutanen da ake nuna wa wariya fiye da kima.
Jin ra’ayi ya nuna cewa kimanin kasha 73% na wadanda aka saurara sun nuna cewa musulmi suna fuskantar matsi da kuma nuna banbanci da wariya, yayin da wasu kuma kimanin kasha 52% suke ganin cewa shi kansa addinin muslunci yana karfafa ayyukan tashin hankali.
Amma da dama daga cikin wadanda aka ji ra’ayoyinsu wadanda suka san wasu musulmin kuma suka mu’amala da su sun yi watsi da ra’ayin cewa musulunci shi ne addinin da ke karfafa gwiwa wajen yada ayyukan tashin hankali, domin kuwa sun san musulmi masu son zaman lafiya da kyakkyawar dabia.
Wannan jin ra’ayin jama’a dai ya hada mutane kimanin 1000 ne, kuma kimanin musulmi miliyan 6 zuwa miliyan 8 ne suke rayuwa a cikin fadin kasar Amurka, amma saboda rashin saninsu hakan ya sanya mafi yawan al’ummar Amurka ba ta da wata masaniya dangane da addinin muslunci baki daya.