IQNA

Babban Malamin Azhar Ya ce Rashin Sanin Hukunci Shi Ne Dalilin Yaduwar Ta'addanci

19:17 - February 28, 2015
Lambar Labari: 2910954
Bangaren kasa da kasa, babban malamin cibiyar Azahar Sheikh Ahmad Tayyib ya bayyana hukuncin day an ta'adda suke yankewa da cewa rashin sanin hukunci da addini shi ne babban dalilin abin da suke aikatawa.

Kamanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadawa na yanar gizo na jaridar Al-watan cewa, Ahmad Tayyib babban malamin cibiyar Azahar ya bayyana hukuncin da 'yan ta'adda suke yankewa da cewa rashin sanin hukuncin addini shi ne babban tushen ta'addancinsu.
Malamin ya ci gaba da cewa bayyana ayyukan ta'addanci a cikin wannan zamani yana da alaka da irin mummunar akidar da aka samar ne tun wasu karnoni da suka gabata, wadanda suke da alaka da fatawoyin kafirta musulmi tare da halastar da jininsu saboda banbancin fahimta kawai tsakaninsu da wasu.
Sheikhul Azhar ya ci gaba da cewa nauyi day a rataya kan malaman addinin muslunci da su mike wajen wayar da kan sauran mabiyansu da am al'umma baki daya, domin kwance kullin da aka kulla a cikin wanann mummuna akida ta kafirta musulmi, wadda kuma sakamakon abin da take dauke das hi ne ake ganin bayyana irin wadannan munan ayyka na ta'addanci da sunan muslunci.
Wasu daga cikin ayyukan da yayan kungiyoyin yan ta'adda suke aikata suna fakewa ko dogara da irin fatawowin da suka samu a cikin littafan malaman da suka gabata da ke dauke da akidar kafirta musulmi tun karnonin da suka gabata, daga ciki kuwa har da fatawowin malamin da ake kira shehin muslunci day a rayu a lokacinsa.
Malamin ya ce wadanda suke aikata wannan danyen ba su wakiltar al’ummar musulmi a abin da suke yi, ko da kuwa sun fake da wasu fatawoyi na  wasu malamai da suke kafirta muuslmi bisa son ransu wadanda suka gabata, wannan shi ne musulunci ba, kuma basu wakiltar al’ummar musulmi balanta musulunci.
2909829

Abubuwan Da Ya Shafa: azhar
captcha