IQNA

ISESCO Ta Yi Allawadai da Kone Majami'a Da Yahudawa Suka Yi

19:20 - February 28, 2015
Lambar Labari: 2910956
Bangaren kasa da kasa, Abdulazi Bin Usman Al-Tuwaijari shugaban kungiyar bunkasa harkokin ilimi da a'adu ta kasashen musulmi ISESCO ya yi Allawadai da kai harin da yahudawan sahyuniya suka yi kan majami'a.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na ISESCO cewa, shugaban kungiyar ya yi Allawadai da kakakusar murya dangane da kai harin da yahudawan sahyuniya suka yi kan majami'ar mabiya addinin kirista.
Ya ci gaba da cewa wannan mataki dai wanda ba shi ne na farko ba kuma ba zai zaman a karshe ba, ya zo ne a lokacin da yahudawan masu tsattsauran ra’ayi suke ci gaba da zafafa hare-harensu babu kakkautawa a kan palastinawa musulmi da kuma mabiya addinin kirista ba tare da wani banbanci a tsakani.
Su dai wadannan yahudawan Isra’ila dai suna aikata hakan tare da cikakken goyon bayan haramatacciyar gwamnatinsu, da ke basu kariya a kowane lokaci suke aikata irin wannan barna da ta’asa kan palastinawa masarra kariya.
Al-tuwaijari ya caccaci kasashen da suke raya cewa suna kare hakkokin bil adama  akasashen turai su ne kan gaba wajen mara baya ga irin wadannan ayyuka na ta’addancin Isra’ila kan sauran al’ummomi masu rauni, ya ce dole a dauki dukkanin matakai domin takawa irin wadannan bakaken ayyuka birki.
2908684

Abubuwan Da Ya Shafa: isesco
captcha