IQNA

Ministocin Harkokin Waje Na Kasashen Musulmi Za sSu Yi Zaman Kan Kyamar Musulmi

23:28 - March 01, 2015
Lambar Labari: 2915454
Bangaren kasa da kasa, ministocin harkokin wajen kasashen musulmi zasu gudanar da wani zama a kasar Kuwait domin tattauna hanyoyin yaki da kyamatar mabiya addinin muslunci a kasashen duniya.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Ina cewa, Tareq Bukhait kakakin kungiyar kasashen musulmi ya bayyana cewa nan da watanni biyu masu zuwa ministocin harkokin wajen kasashen musulmi zasu gudanar da wani zama a kasar Kuwait domin tattauna hanyoyin yaki da kyamatar mabiya addinin muslunci a kasashen turai musamman.
Ya ci gaba da cewa wannan zaman taro da za a gudanar a kasar Kuwait, ya yi kamada irinsa na 2011, amma wannan zai mayar da hankali kan irin matakan da ya kamata a dauka a mataki na kasa da kasa domin fuskantar irin barazanar da musulmi suke fuskanta a wasu kasashe, tare da nuna msu kyama musamman a wadannan lokuta da ake batun ta’addanci, tare da sanin hanyoyin shawo kan wannan matsala.
Haka nan kuma a cikin shekara ta 2012 an yi wasu taruka dangane da irin abubuwan da suke faruwa a cikin wasu kasashen larabawa, da sanin hanyoyin da za a fuskanci lamarin, wanda kuma shi ne babban ummul habaisin dukkanin abubuwan da suke faruwa a halin yanzu na dagula kasashen musulmi tare da rusa su.
Majalisar dinkin duniya ta nuna cikakken goyon bayanta dangane da gudanar da wannan zama, wanda wakilinta zai samu halarta, domin domin daukar matakin da ya dace da kaidoji da dokoki na kasa da kasa wajen kare hakkokin musulmi a cikin kasashen turai.
2913261

Abubuwan Da Ya Shafa: oic
captcha