Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Alfajr cewa, Mohyiddin Afifi shugaban bangaren bincike na cibiyar Azahar da ke kasar Masar ya bayyana cewa dukkanin addinan da aka safkar daga sama tashin hankali baya daga cikin abin da suka amince da shi.
Shi ma a nasa bangaren babban malamin cibiyar Azahar ya bayyana hukuncin da 'yan ta'adda suke yankewa da cewa rashin sanin hukuncin addini shi ne babban tushen ta'addancinsu.
Shehin malamin ya ci gaba da cewa bayyana ayyukan ta'addanci a cikin wannan zamani yana da alaka da irin mummunar akidar da aka samar ne tun wasu karnoni da suka gabata, wadanda suke da alaka da fatawoyin kafirta musulmi tare da halastar da jininsu saboda banbancin fahimta kawai tsakaninsu da wasu sauran addinai.
Ya ci gaba da cewa nauyi day a rataya kan malaman addinin muslunci da su mike wajen wayar da kan sauran mabiyansu da am al'umma baki daya, domin kwance kullin da aka kulla a cikin wanann mummuna akida ta kafirta musulmi, wadda kuma sakamakon abin da take dauke das hi ne ake ganin bayyana irin wadannan munan ayyka na ta'addanci da sunan addini.
Daga cikin ayyukan da yayan kungiyoyin yan ta'adda suke aikata suna fakewa ko dogara da irin fatawowin da suka samu a cikin littafan malaman da suka gabata da ke dauke da akidar kafirta musulmi tun karnonin da suka gabata
Ya ce wadanda suke aikata wannan danyen ba su wakiltar al’ummar musulmi a abin da suke yi, ko da kuwa sun fake da wasu fatawoyi na wasu malamai da suke kafirta muuslmi bisa son ransu wadanda suka gabata, wannan shi ne musulunci ba.
2920138