IQNA

Mu Yi Kokari Mu Kusanto Da Fahimitar Addinai Maimakon Nisanta Da Juna

16:04 - March 07, 2015
Lambar Labari: 2941599
Bangaren kasa da kasa, akarshen taro cibiyar yada al’adun muslunci karo na shida da aka gudanar a kasar Lebanon an yi kira da a kusanto da fahimta tare da sauran addinai.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya akalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na bangaren hulda da jama’a na cibiyar yada al’adun mslunci cewa, Abu Zar Ibrahim Turkman ya bayyana cewa, dole ne  ayi aiki tukuru domin kara kusanto sa dauran addinai da samun fahimtar juna, maimakon yin wasu abubuwa da za su kara nisanta su daga addinin muslunci.
Ya ci gaba da cewa bayyana ayyukan ta'addanci a cikin wannan zamani yana da alaka da irin mummunar akidar da aka samar ne tun wasu karnoni da suka gabata, wadanda suke da alaka da fatawoyin kafirta musulmi tare da halastar da jininsu saboda banbancin fahimta a kan wasu mas’aloli.

Haka nan kuma nauyi da ya rataya kan malaman addinin muslunci da su mike wajen wayar da kan sauran mabiyansu da am al'umma baki daya, domin kwance kullin da aka kulla a cikin wanann mummuna akida ta kafirta musulmi, wadda kuma sakamakon abin da take dauke da shi ne ake ganin bayyana irin wadannan munan ayyka na ta'addanci da sunan muslunci.

A bangare guda kuma ya yi kakkausar suka da yin Allawadai dangane da yadda wasu suke ta kokarin yada kiyayya da mabiya mazhabar shi’a a cikin kasashen larabawa a wannan lokaci, da nufin haifar da fitina da sunan banbancin mazhaba.
Malamin ya ci gaba da cewa duk inda aka samu wani mutum ko da yana kiran kansa malamai a cikin al’ummar musulmi kuma yana yada duk abin da zai haifar da fitina da rashin fahimtar juna tsakanin al’ummar musulmi, to tabbas wannan mutumin ko ya sani ko bai sani ba yana yi ma makiya musulunci aiki ne kai tsaye.
2938200

Abubuwan Da Ya Shafa: taro
captcha