Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Yaum Sabi cewa, Najeh Ibrahim a lokacin da yake jawabi a jamai'ar Asyut ta kasar Masar ya bayyana cewa 'ayn Takfiriyya sun saki hanyar addinin muslunci sun kama hanyar bata mai nisa matukar dai bas u dawo zuwa koyar muslunci ta gaskiya ba.
Malamin ya ci gaba da cewa bayyana ayyukan ta'addanci a cikin wannan zamani yana da alaka da irin mummunar akidar da aka samar ne tun wasu karnoni da suka gabata, wadanda suke da alaka da fatawoyin kafirta musulmi tare da halastar da jininsu saboda banbancin fahimta kawai tsakaninsu da wasu.
Ya ci gaba da cewa nauyi day a rataya kan malaman addinin muslunci da su mike wajen wayar da kan sauran mabiyansu da am al'umma baki daya, domin kwance kullin da aka kulla a cikin wanann mummuna akida ta kafirta musulmi, wadda kuma sakamakon abin da take dauke das hi ne ake ganin bayyana irin wadannan munan ayyka na ta'addanci da sunan muslunci.
A bangare guda kuma ya bayyana cewa abin takaici ne yadda wasu daga cikin ayyukan da yayan kungiyoyin yan ta'adda suke aikata suna amafani fatawowin da suka samu a cikin littafan malaman da suka gabata da ke dauke da akidar kafirta musulmi.
Daga karshe ya ce dole ne malamai su mike da fadakrwa da wayar da matasa musulmi musamman wadanda ake yaudararsu domin sanin muslunci na gaskiya.